Da Ɗumi Ɗuminsa! Jakadan Faransa a Nijar ya fita daga kasar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai kwashe dakarun kasar daga Nijar nan da karshen shekarar da muke ciki.

Jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar ya fice daga kasar da sanyin safiyar Talata, a cewar wasu majiyoyin tsaro guda biyu, kusan wata guda bayan sojojin da suka yi juyin mulki sun ba shi wa’adin fita daga kasar.

A watan jiya ne sojojin kasar suka bai wa jakada Sylvain Itte umarnin fita daga kasar bayan “ya ki amsa gayyatar ma’aikatar harkokin waje don halartar taron” da aka gayyace shi da kuma “wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar”.

Sai dai tun daga wancan lokacin jakadan bai fita ba kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi zargin cewa sojojin kasar ta Nijar sun yi “garkuwa” da shi.

Reuters

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *