Da Ɗumi Ɗuminsa! Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Zartarwa ta 14

Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata doka ta Gudanar da Sauye-sauyen Shugaban Kasa.

Wannan ci gaban ya fito ne a cikin wata sanarwa ta hanyar ingantaccen shafinsa na Twitter ranar Alhamis.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ya amince da kafa kwamitin mika mulki na shugaban kasa, wanda sakataren gwamnatin tarayya, SGF zai jagoranta.

Buhari ya rubuta: “Na rattaba hannu kan dokar zartarwa mai lamba 14 na shekarar 2023 kan Saukakewa da Gudanar da Canjin Shugaban Kasa.

Sabuwar Dokar Zartarwa ta kafa tsarin doka don mika mulki gadan-gadan daga wannan Gwamnatin Shugaban kasa zuwa waccan.

“Na kuma amince da kafa kwamitin mika mulki na shugaban kasa, wanda sakataren gwamnatin tarayya (SGF) zai jagoranta, don saukakawa da kuma gudanar da shirin mika mulki ga shugaban kasa a 2023.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *