DA DUMI-DUMI: Aisha Buhari ta umarci ma’aikatanta da su tafi hutu, yayin da ake ta rade-radinta da samun juna biyu

 DA DUMI-DUMI:
 Aisha Buhari ta umarci ma’aikatanta da su tafi hutu, yayin da ake ta rade-radinta da  samun juna biyu. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel

Mai dakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Aisha, ta umurci dukkan ma’aikatanta da su ci gaba da hutu. 

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin kiwon lafiya a ofishin uwargidan shugaban kasa Mohammed Kamal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. 

lokacin da suka halarci taron hadin gwiwa na Turkiyya na Afirka karo na 3. Hotunan uwargidan shugaban kasar da fadar shugaban kasar ta fitar bayan tafiyar ta janyo ce-ce-ku-ce a kan juna biyu, yayin da aka nuna hotonta yayi kama da mai ciki. 

Best Seller Channel 

Jaridar The PUNCH ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Aisha, Aliyu Abdullahi; da kuma wani mataimaki da ke aiki tare da uwargidan shugaban kasa, Suleiman Haruna, amma hakan ya ci tura. 

Yayin da ba a samu wayar Abdullahi ba, kuma har zuwa lokacin da aka buga labarin ba a amsa sakon da aka aika zuwa layinsa ba, Haruna ya ki cewa komai kan lamarin lokacin da wakilinmu ya tuntube shi. 

Wata sanarwa Kuma, ta ce, za a rufe ofishin uwargidan shugaban kasa a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai zuwa. 

Don haka, ana buƙatar dukkan ma’aikatan da su ci gaba da hutu, har sai an samu sanarwa.