Da Dumi Duminsa!
Wata Babbar Kotun Tarayya Ta Ai ke Da Atiku Abubakar Gwandu Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya.
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta aike da Atiku Abubakar Gandu wani Dan kasuwa gidan gyaran hali da tarbiyya, bisa zarginsa da karya tare da raba gurbatattun man Ammasco da IBCON na motoci.
Mai shari’a Kolawole Omotoso ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin ne biyo bayan gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume guda 7 da suka hada da samar da kayayyakin da ba su da inganci da kuma sauya musu suna domin rabawa masu saye da sunan ingantaccen.
Mai magana da yawun hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya (SON). Maji Aileku, ya fitar a ranar Talata.
Best Seller Channel
Sanarwar ta bayyana, babban mai shigar da kara na hukumar SON, Kuma Moor (Esq.), ya bayar da hujjar cewa wanda ake tuhumar suna ta farautarsa tun a shekarar 2018, kuma duk kokarin kama shi a baya ya ci tura, don haka ya kamata a hana wanda ake tuhuma beli kamar yadda ya saba, Mai yuwa ne ya tsere idan aka bashi beli.
Jaridar Alkiblah ta rawaito “Atiku ya ki amsa zargin da ake masa, kuma Kotu taki amincewa da bukatar belin da lauyansa ya yi, inda alkalin kotun ya ba da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake zaman,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ofishin hukumar SON na jihar Sokoto da SON, da sa ido (SIM) tare da hadin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) bisa wani rahoton bayanan sirri da suka samu, sun kai wani sumame a harabar Atiku Abubukar Gwandu a watan Nuwambar da ya gabata.
Best Seller Channel
Maji ya cigaba da cewa, “a cikin haka ne rundunar ‘yan sandan ta gano kayayyakin da aka yi amfani da su wajen samar da gurbatattun man injin da ba su da inganci tare da robobi masu sunan Ammasco da man Injin IBCON a jikinsu”.
Laifukan da ke karkashin sashe na 26 (2) na dokar hukumar SON 14:2015.
Hukumar SON ta yi zargin “Wadanda ake tuhumar, sun gudanar da rabon mai na Ammasco da IBCON da suka lalata ta, wanda ya canza inganci, sinadari, yanayi da ingancin man injin, da niyyar sayar da makamancin haka ga masu saye.
Laifin da za a hukunta shi a karkashin sashe na 1 (1) 18) na dokar laifuffuka daban-daban CAP M17 LFN 2005, da sauran tuhume-tuhume.
An dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2022 Inji Sanarwar.