Da Dumi Duminsa! Gwamnatin Kano Ta Haramta Haya Da Jirgin Ruwa A Bagwai

 Gwamnatin jihar Kano ta sanar da haramta amfani da jiragen ruwa wajen jigilar fasinjoji a kogin Bagwai-Badau a karamar hukumar Bagwai ta jihar

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da haramta amfani da jiragen ruwa na kasuwanci wajen jigilar fasinjoji a kogin Bagwai-Badau a karamar hukumar Bagwai ta jihar. 
Umarnin ya biyo bayan hatsarin kwale-kwalen ne yayi a ranar Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 29 a kauyen Badau da ke karamar hukumar. 

 Jaridar Nigeria Tracer ta rawaito Malam Muhammad Garba, ya ce  gwamnati ta samar da motocin bus guda biyu na jigilar fasinja tsakanin Badau da Bagwai, yayin da kuma za a sayo sabbin jiragen ruwa guda ukudon Samar Da  ingantaccen sufurin ruwa a yankin.

 Ya ce ana sa ran kaddamar da wasu matakan da suka dace a lokacin da kwamitin binciken da gwamnatin jihar ta kafa ya mika rahotonsa don aiwatar da shi.

Best seller Channel

Slide Up
x