Da Dumi Duminsa! Gwamnatin Kano Ta Haramta Sha Da Siyar da Shisha A Kano

 Da Dumi Duminsa Gwamnatin Kano Ta Hana Siyarwa da Shan Shi Sha a kano da Hana Cakuduwar Maza da Mata a guraren cin abinci wato (Joint) 

Hon Yusuf Ibrahim Lajawa shine  Shugaban Hukumar Shakatawa  Da Yawon Bude Ido Ta Jihar Kano Tourism Board, ya Bayyanawa Best seller Channel a yammacin yau Talata bayan wani zama da Hukumar tayi da shugaban masu Hotels, da masu Restaurant, da masu Suya Sport, da masu Joint, da masu Bakery, da kuma masu Event Center tare da masu gidajen kallo da Sauransu

Shugaban Hukumar ya tabbatar da doka da majalisar Jihar Kano Ta tabbatar,  Kuma Mai Girma Gwamnan Kano Dr Umar Abdullahi Ganduje ya sakawa hannu na hana Sha da siyar da Shi Sha a jihar Kano da hana haduwar Maza da Mata a wuraren Shakatawa Da Kuma hana Bawa Yara yan kasa da shekara 18 Daki a hotel.

Ga cikakkiyar tattaunawar nan a video 

Slide Up
x

3 Replies to “Da Dumi Duminsa! Gwamnatin Kano Ta Haramta Sha Da Siyar da Shisha A Kano

Comments are closed.