Da Dumi Duminsa!
Gwamnatin Kano Za Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Sufuri A Jihar.
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabon tsarin sufuri a cikin babban birnin jihar nan ba da jimawa ba.
Shugaban Hukumar karota ta jihar Kano, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yajin aikin da masu baburan adaidaita sahu suka fara a jihar.
Ya ce Gwamnati za ta kaddamar da sabon tsarin sufurin ne saboda muna son a duba yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda ake yi a yanzu.
Best Seller Channel
“Tuni dai shirye-shirye sun kai ga samar da ababen hawa.
Yan Adaidaita sun tafi yajin aiki saboda sabunta takardar izinin aiki.
Gwamnatin jihar ta rage kudin daga N100,000 zuwa N8,000, domin samun damar biya.
Duk da cewa wasu sun biya, wasu kuma ba sa son biyan kudaden shiga na gwamnati, da doka ta ce su biya., ba sa son mutunta doka, suna ganin tsaron da suke samu ba don komai ba ne.
Ba ni da wani ikon cewa dole ne su koma aiki.
“Duk da haka, ba su da wani hurumi da za su ce mini kada in nemi bayaninsu kuma kada in kama su da daukar matakin da ya dace a kansu,” inji shi.
Best Seller Channel
Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati ta damu da tsaro ba wai batun kudaden shiga bane kawai kamar yadda suke tunani.
“Wasu daga cikinsu suna ci gaba da aikata laifuka tare da masu baburan, ba sa son yin rajista,” in ji shi.
Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar da ta taimaka wa wadanda wasu ‘yan baranda suka lalata babura uku a lokacin da suka yanke shawarar kin shiga yajin aikin.