Da Dumi Duminsa! Hukumar Tattara Haraji Ta Kano Ta Rabawa Ma aikatanta Takardar Tuhuma (Query) Sama Da Mutum 200

Shugaban Hukumar Tattara Haraji Ta Kano (KIRS) Ya Rabawa Maaikatansa Takardar Tuhuma (Query) Sama Da Mutum 200

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Best seller channel ta rawaito shugaban hukumar tattara haraji Abdurrazak Datti Salihi ne ya bayar da wannan takardar Tuhuma query a ranar jumaa da ta gabata ya yin rangadi da ya yi a ofis din da misalin karfe 5:20 na yammacin Juma ar.

Takardar da Shugaban ya ba da umarnin rabawa ma’aikatan ta kunshi bayani kamar haka. 

An lura cewa ba ka kan kujera a lokacin da shugaban hukumar ya kawo maka ziyara. ofis a ranar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021

An iske baka man a kan aikinka. 

Bisa la’akari da abubuwan da ke sama, ya kamata ku bayyana dalilin da ya sa Baka nan don za a dau matakin ladabtarwa a kanka. 

Saka hannu kan takarda

SALISU AUWALU a madadin  Chairman


Best Seller Channel 

Da muka tuntubi wasu daga cikin ma aikatan, sun bayyana mana cewar ranar Litinin da Juma a shugaban yayi rangadi bayan karfe 5 na yamma lokacin wasu sun tashi wasu kuma suna wajen aiki a waje duba da cewar aikin nasu yawanci ba na zama bane suna yawace yawace wajen tattara haraji, Iokacin da yazo ba mitune shine ya dau sunayen wadanda suke nan daga bisani wadanda bai same su ba aka bisu da takardar tuhuma (Query) su sama da dari 200

Best seller channel ta tuntubi kakakin yada labarai na hukumar Rabiu Sale a ranar Litinin 3 ga Janairu 2022 ya ce Sai dai a bara talata saboda hutu da ake zai bincika. 

Mun sake tuntubarsa a ranar talata ko me zai ce kan wannan batun? Sai ya ce chairman suna meeting idan sun fito ya gana dashi zai kiramu. 

Kawo lokacin da muka hada wannan rahoton bai ce komai ba. 

Best Seller Channel 

Best seller channel ta tuntubi wani masani a hukumar ma aikata jihar Kano kan halaccin raba takardar tuhuma (Query) da ta kai adadin sama da mutum 200, sai ya ce hakan ba laifi bane, amma sai an bi matakin da ya dace kan wanda ya hada da gargadi da baki, takardar Jan Kunne sannan idan ba aji ba a iya bada takardar tuhuma (Quiry). 

Mun sake tuntubar wata da ta sami wannan takardar tuhumar (Quiry) ko an basu takardar gargadi da jan kunne? 

Ta ce a a takardar tuhuma suka samu sama ta ka.

Slide Up
x