Da Dumi Duminsa! Kotun daukaka kara ta Sanya Rana Kan Yanke hukuncin Rikicin APC A Kano
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ajiye hukunci a karar da bangaren Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC a Kano ya shigar kan bangaren Mal Ibrahim Shekarau.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kotun ta dauki takaitaccen bayani da kuma rashin amincewar bangarorin da ke cikin karar tare da ajiye hukunci ga kararrakin uku.
Idan dai za a iya tunawa, wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta amince da nadin da aka yi na gundumomi da na kananan hukumomi da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar a kan na bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje.
Majalisar ta fitar da Abdullahi Abbas daga bangaren Gwamna Ganduje da Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaba na bangaren Shekarau.
Rashin gamsuwa da hukuncin kotun, bangaren Ganduje ta shigar da kara 3 a kotun daukaka kara.
A ranar Juma’a, Barr. Abdul Fagge ya wakilci wasu daga cikin masu kara yayin da Barr. Nuraini Jimoh SAN, ya wakilci wadanda ake kara
Solacebase ta ruwaito cewa kotun ta ce za a sanar da ranar da za a yanke hukunci ga bangarorin.