Dubun Wani Dalibin Ya Cika, Bayan Da Ya Kyakkyeta Wuyan abokin karatunsa Da Reza

Wani Dalibin Ya Kyakkyeta Wuyan abokin karatunsa Da Reza

Best Seller Channel 

 


Best Seller Channel 

Wani dalibin sakandare ya shiga hannu bayan da yayi da yunkurin kashe wani dan ajinsu ta hanyar yanke masa jiyoyin wuya da reza. 

Dalibin da ya yi wannan danyan aikin dan aji biyu ne na babbar sakandare, kuma a halin yanzu yana hannun ’yan sanda don fadadda bincike. 
Abin  ya faru ne a shahararriyar makarantar nan ta El-Kanmi College of Islamic Theology da ke Maiduguri, a bayan wani dakin kwanan dalibai da dare.

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Dalibin da aka yayyanka,  bai wuce shekara 12 a duniya ba, ya gamu da ibtilabin ne bayan wani dan aji biyu a Babbar Sakandare ya aike shi, shi kuma ya ki zuwa aiken, wato seniority.

Daga baya ne shi wanda ya yi aika aikan ya kira Jibrin wanda aka yiwa ta asar   da tsakar dare zuwa wani wuri da babu kowa, ya sanya reza ya yanke shi a tsakiyar wuyansa, ya kuma yayyanke jijiyoyin wuyan.

Wayewar gari  ne aka tsinci karamin yaron a kwance jina-jina, a galabaice, a bayan dakin kwanan.

Best Seller Channel 
Take aka wuce da yaron zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, domin ceto rayuwarsa.

Daga bisani hukumar makarantar ta kira ’yan sanda suka yi awon gaba da wanda ake zargin zuwa bangaren binciken Manyan Laifuka na rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno.

 Wani malamin makarantar da ya bukaci Aminiya ta boye sunansa ya yi zargin yawan rashin tsawatarwa da kuma ladabatar ga dalibai, ya faru ne saboda dan na Goro da malaman suke samu daga hannun iyayen yaran

Best Seller Channel 

Malamin ya bayyana takaicinsa game da abin da ya faru, sannan kuma abin da ya kira halayyar wasu malaman makarantar ga daliban kwana ta rashin kyautawa, wadanda yawancinsu ’ya’yan manyan mutane ne. 

Mahaifin Jibrin ya bukaci a sanar da duniya halin da ake ciki domin a musu adalci, da wannan muke kira ga Maigirma Gwamnan jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya san abinda yake faruwa tare da daukar matakin gaggawa akan shugaban makarantar bisa kokarinsa na rufe maganar. 

Best Seller Channel 

Ga. Yadda sunan Best Seller Channel ya koma Yan uwa masu albarka. 

Slide Up
x