Da Dumi Duminsa! Sarkin Filato Ya Sheki Iskar Yanci Daga Masu Garkuwa

 Masu garkuwa da mutane sun sako Sarkin Filato kwanaki biyar bayan sace su. 

Best Seller Channel 

An sako Basaraken gargajiya da aka yi garkuwa da shi a Jihar Filato, Charles Mato Dakat. 

An yi garkuwa da Dakat wanda shi ne Basarake a masarautar Gindiri a karamar hukumar Mangu a jihar lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari fadarsa a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 1 na safe.

 Wadanda suka yi garkuwa da shi sun yi tuntubar ‘yan uwa bayan ‘yan kwanaki inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 500 kafin su sako sarkin. 


Best Seller Channel 

Sai dai an tattaro cewa daga karshe basaraken ya sake samun ‘yancinsa da sanyin safiyar Juma’a. 

Jaridar PUNCH ta rawaito, da ta tabbatar da sakin Dakat din a ranar Juma’a, inda ya ce, “Allah ya karbi addu’o’inmu.

 An saki Mai Martaba Sarki Charles Mato Dakat cikin koshin lafiya, da aka tambaye ta ko nawa aka biya masu garkuwa da mutane domin a sako sarkin, majiyar ta ce, “Abin da zan iya fada muku shi ne rayuwa ta fi kudi. Na gode da addu’o’in ku, ƙarfafawa da goyon baya. 

Best Seller Channel 

Majiyar ta kara da cewar godiya ta tabbata ga Allah, manyan abubuwan da ya yi kuma zai ci gaba da yi.” 

Slide Up
x