Gwamna Ganduje Yace Sabuwar Shekara Ta Sulhu Ce! Sulhu Alkhairi ne
Best Seller Channel
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata sabuwar shekara ta 2022 ta kawo sabon zaman lafiya da sulhu a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyun siyasa a jihar da ma kasa baki daya.
A sakon sabuwar shekara ga al’ummar jihar wanda Muhammad Garba kwamishinan yada labarai ya fitar, gwamnan ya ce daga dukkan alamu abubuwan da suka faru a Kano na iya kawo wani sabon salo a tarihin siyasar jihar.
Best Seller Channel
Ya kara da cewar taron, wanda ya ga ‘yan siyasar Kano sun jaddada bukatar yin sulhu, ya jawo hankulan jama’ar jihar Kano da ke kishin ganin an samar da zaman lafiya da sulhu da ake bukata domin a samu ci gaba mai inganci a fagen siyasa. da al’umma gaba daya.
Ganduje ya nuna matukar damuwa kan yadda ake ta Fama da tabarbarewar tsaro a fadin kasar baya ga mummunar fatara da ake fama da ita sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a kasar.
Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa duk da kalubalen da ake fuskanta gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da kokarin ganin an aiwatar da manufofinta da shirye-shiryenta yadda ya kamata domin rage radadin jama’a.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa, wadda kasafin kudin 2022 ke ba da fifiko wajen kammala ayyuka, ta kuduri aniyar kyautata wa al’umma ta hanyar kawo sauyi a yankunan karkara da kuma shirye-shiryen karfafa tattalin arziki.
Best Seller Channel
Gwamna Ganduje ya taya al’ummar kasar murnar shiga sabuwar shekara,ya kuma yi kira da a hada kai da yi wa kasa addu’a musamman malaman addini su rika wa’azin zaman lafiya, hakuri da juna a cikin kalubalen da ake fuskanta.
Allah ya sada mu da alheranta ameen.