Da Dumi Duminsa: Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeton ‘Yan Sanda IGP Egbetokun

IMG 20260224 WA0122

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sallami Kayode Egbetokun daga muƙaminsa na Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).

Manyan jami’an ‘yan sanda da kuma majiyoyi daga Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda sun tabbatar da wannan sanarwa.

Tuni aka naɗa Tunji Disu, wanda a yanzu yake riƙe da muƙamin Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda (FCID Annex) da ke Alagbon a Lagos, a matsayin wanda zai gaji Egbetokun.

Wata majiya ta bayyana cewa Egbetokun ya je Fadar Shugaban Ƙasa jiya inda aka umurce shi ya shirya takardun miƙa mulki, kuma tuni ya riga ya kammala shiri domin miƙa ragamar aiki ga Tunji Disu.

Majiyar ta kuma bayyana Egbetokun a matsayin wanda ake zargi da rashin ƙwarewa da nuna karfin iko fiye da kima, tare da cewa mulkinsa cike yake da cece-kuce.

Rahotanni sunce Shugaban Ƙasa ya ba shi shawarar ya sauka daga muƙaminsa domin ya mai da hankali kan jinyar cutar da yake fama da ita mai alaƙa da ƙoda.

Wasu bayanai sun nuna cewa cire Egbetokun ya samu karɓuwa sosai a tsakanin jami’an ‘yan sanda, inda aka ce sun yi murna da jin labarin a ranar Litinin.

Saidai kuma wasu bayanan karkashin kasa sun ce ana zargin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, na son ya ci gaba da zama a muƙaminsa, Saidai Shugaban ya nace kan shawarar cire shi.

Zaman Egbetokun a matsayin IGP ya fuskanci cece-kuce da dama, musamman batun tsawaita wa’adinsa fiye da shekarun ritaya da dokokin aikin ‘yan sanda suka tanada, lamarin da ya janyo muhawara kan yiwuwar karya ƙa’idoji.

Haka kuma, an zargi mulkinsa da nuna son kai da fifita wasu na kusa da shi, musamman dangane da karin girma cikin gaggawa ga wasu jami’ai. Daga cikin waɗanda aka ambata har da Bukola Yemisi Kuti, babbar jami’arsa ta musamman, wadda masu suka ke zargin tana da alaka ta ƙashin kai da shi.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da batun wasu kuɗaɗen tsaro na jihar Anambra har naira miliyan 100 da ake zargin sun kai ta hannun Victor, ɗan Egbetokun. Masu suka sun nuna damuwa kan yiwuwar karkatar da kuɗaɗen gwamnati don amfanin kai, zarge-zargen da suka haddasa matakan shari’a masu tsauri daga hukumomin ‘yan sanda kan ‘yan jarida da masu fafutuka da suka ruwaito labarin.: Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeton ‘Yan Sanda IGP Egbetokun

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sallami Kayode Egbetokun daga muƙaminsa na Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).

Manyan jami’an ‘yan sanda da kuma majiyoyi daga Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda sun tabbatar da wannan sanarwa.

Tuni aka naɗa Tunji Disu, wanda a yanzu yake riƙe da muƙamin Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda (FCID Annex) da ke Alagbon a Lagos, a matsayin wanda zai gaji Egbetokun.

Wata majiya ta bayyana cewa Egbetokun ya je Fadar Shugaban Ƙasa jiya inda aka umurce shi ya shirya takardun miƙa mulki, kuma tuni ya riga ya kammala shiri domin miƙa ragamar aiki ga Tunji Disu.

Majiyar ta kuma bayyana Egbetokun a matsayin wanda ake zargi da rashin ƙwarewa da nuna karfin iko fiye da kima, tare da cewa mulkinsa cike yake da cece-kuce.

Rahotanni sunce Shugaban Ƙasa ya ba shi shawarar ya sauka daga muƙaminsa domin ya mai da hankali kan jinyar cutar da yake fama da ita mai alaƙa da ƙoda.

Wasu bayanai sun nuna cewa cire Egbetokun ya samu karɓuwa sosai a tsakanin jami’an ‘yan sanda, inda aka ce sun yi murna da jin labarin a ranar Litinin.

Saidai kuma wasu bayanan karkashin kasa sun ce ana zargin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, na son ya ci gaba da zama a muƙaminsa, Saidai Shugaban ya nace kan shawarar cire shi.

Zaman Egbetokun a matsayin IGP ya fuskanci cece-kuce da dama, musamman batun tsawaita wa’adinsa fiye da shekarun ritaya da dokokin aikin ‘yan sanda suka tanada, lamarin da ya janyo muhawara kan yiwuwar karya ƙa’idoji.

Haka kuma, an zargi mulkinsa da nuna son kai da fifita wasu na kusa da shi, musamman dangane da karin girma cikin gaggawa ga wasu jami’ai. Daga cikin waɗanda aka ambata har da Bukola Yemisi Kuti, babbar jami’arsa ta musamman, wadda masu suka ke zargin tana da alaka ta ƙashin kai da shi.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da batun wasu kuɗaɗen tsaro na jihar Anambra har naira miliyan 100 da ake zargin sun kai ta hannun Victor, ɗan Egbetokun. Masu suka sun nuna damuwa kan yiwuwar karkatar da kuɗaɗen gwamnati don amfanin kai, zarge-zargen da suka haddasa matakan shari’a masu tsauri daga hukumomin ‘yan sanda kan ‘yan jarida da masu fafutuka da suka ruwaito labarin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *