shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti Paul Omotosho ya rasu.
Omotosho ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
An tattaro daga makusantansa cewa, dan siyasar da aka haifa Imesi-Ekiti ya taka rawa sosai a wasu tarurrukan siyasa a ranar Litinin.
An ce ya yi korafin rashin lafiya a ranar Talata, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibitin gwamnati da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar, inda daga baya ya rasu.
Idan zaku tuna cewa an yi garkuwa da marigayi Omotosho ne a watan Yulin 2023 kuma an sake shi bayan kwanaki biyar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk