Da Yiwuwar Samun Ragi A kuɗin Aikin Hajji Sakamakon Faɗuwar Darajar Dalar Amurka — Shugaban NAHCON

FB IMG 1713460483927

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.

Alfijir Labarai ta rawaito Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.

“Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1,000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuɗinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai rarar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata mu mai da maka. Ba mu jira tana ta yin ƙasa ba. To idan kuma ta ƙara yin sama fa?” In ji Jalal Arabi.

Ya ƙara da cewa “indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan haƙƙin kowa ba da izinin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar.”

To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya bai faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.

A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.

A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *