Da Ɗumi Ɗuminsa! Shugaba Buhari Ya Sauke shugaban Hukumar NASENI

Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci mataimakin shugaban hukumar  kula da harkokin kimiyya da fasaha ta kasa (NASENI), Farfesa Mohammed Sani. Haruna, da gaggawar barin ofis.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Farfesa Haruna ya mika ofishin nasa ga babban jami’i na hukumar.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan sauya wa’adin aiki da shugaban kasa ya yi daga ranar 2 ga Afrilu, 2023 zuwa 2 ga Afrilu, 2025 saboda yadda EVC ta kammala wa’adi biyu na shekara biyar kowacce a kungiyar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan ofishin yada labarai na SGF Willie Bassey ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ya ce shugaban ya yaba da gudummawar da Farfesa Haruna ya bayar wajen bunkasa bangaren samar da ababen more rayuwa a bangaren tattalin arziki, tare da yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *