Kotu Ta Bayar Da Umarnin Yanka Wani Zakara A Kano


Alfijr ta rawaito Kotun Majistire da ke zamanta a harabar gidan Murtala dake Kano, ta bai wa wani magidanci Isyaku Shu’aibu da ke unguwar Ja’en umarnin yanka Zakaransa.

Hakan na zuwa ne lokacin da maƙwabcin mai Zakaran Malam Yusuf Muhammad ya shigar da ƙara a kotun, yana mai da’awa cewa Zakaran ya na hana shi yin barci saboda yawan yin Cara.

Bayan karanta wa wanda ake ƙara tuhuma nan take ya amsa, yana mai cewa, batun yawan yin Cara da aka ce gaskiya ne, sai dai ya roƙi kotun da ta ɗaga masa ƙafa zuwa ranar bikin “Good Friday” zai yanka shi a ranar.

A nan ne alƙalin kotun mai shari’a Halima Wali ta amince da roƙon nasa inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a juma’a mai zuwa watau ranar “Good Friday” kamar yadda ya roƙa.

Freedom Radio

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *