Alfijr ta rawaito wasu daliban jami’ar sun kone kurmus. , ranar Asabar.
Rahotanni sun ce daliban sun mutu ne a lokacin da wata motar safa da ke dauke da su a kan hanyarsu ta zuwa jihar Taraba daga Fatakwal ta yi hatsari kuma ta kama su.
An ce daliban za su je gida ne domin hutun zabe a lokacin da hatsarin ya afku.
Wani shaidar gani da ido ya ce an garzaya da wasu dalibai goma da suka samu kubuta daga motar bas din da ta kone zuwa asibitin koyarwa na Alex Ekwueme da ke jihar Ebonyi domin kula da lafiyarsu.
Daya daga cikin iyayen marigayin mai suna Grace Usman Ezra, ya bayyana alhininsa game da rashin ‘yarsa a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana cewa bai taba tunanin tura ‘yarsa Jami’ar Madonna zai yi sanadiyar mutuwarta ba.
Ya kuma mika addu’a ga dalibai goma da suka tsira daga hatsarin, tare da yi musu fatan samun lafiya cikin gaggawa, tare da rokon Allah ya jikan dukkan iyayen da suka rasa ‘ya’yansu a hadarin.
Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba, amma rahotanni sun ce an fara gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇