Dalilin Da Yasa Na Saka Wuta A Masallaci – In Ji Wanda ake Tuhuma

IMG 20240515 WA0071

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da kama wanda ake zargi da saka wuta a wani masallaci da sanyin safiyar yau a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito kwamishinan ‘yan sandan jihar Usaini Gumel, ya shaidawa Kamfanin Dallancin Labarai na Ƙasa NAN a wata hira ta wayar tarho a ranar Laraba cewa an kama wani matashi mai shekaru 38 Shafi’u Abubakar kan lamarin.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin kai hari masallacin ne saboda takaddamar da aka dade ana yi tsakanin dangi kan rabon gado.

“A ranar 15 ga watan Mayu, 2024, da misalin karfe 5:20 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton fashewar wani abu a wani masallaci da ke kauyen Gadan a lokacin sallar asuba, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

“Nan da nan, an tura wata tawagar jami’an tsaro, ciki har da kwararru masana abubuwan fashewar sinadarai da Radiyo da kuma Nukiliya (EOD-CBRN), zuwa wurin.

“An garzaya da mutane ashirin da hudu da suka hada da maza 20 da yara hudu wadanda suka samu raunuka daban-daban zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano domin yi musu magani,” inji shi.

CP ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa fashewar bam ne ya tashi kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

Ya ce ‘yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su fitar da karin bayani nan gaba kadan.

Sai dai yanzu haka 1 Daga Cikin Mutanen Da Aka Cinna Wa Wuta A Masallaci A Kano Ya Rasu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *