Daga Aminu Bala Madobi
Alkaliyar wasa ƴar ƙasar Jamus ta bawa ɗan wasan Turkiyya Katin kora akan hanyar sa ta fita daga cikin fili a yayin da ɗan wasan ya kalleta yace mata:
“Kamata yayi yanzu ace kina ɗakin Girki wajen dafa Abinci”.
Rahotonni sunce Alƙaliyar wasan ta rubuta wannan kalmar da ya faɗa mata a cikin rahoton wasan ga FIFA, Kuma hakan yasa FIFA ta dakatar da ɗan wasan na tsawon wasanni Biyar.
Binciken Jaridar Alfijir Labarai ya nuna cewa cikin hukuncin da akayi masa an bashi umarnin dole ya Alƙalanci busa wasan mata guda ɗaya.
Lokacin da yake biyayya ga hukuncin na FIFA akan ya busa wasan mata, Ɗan wasan na Turkiyya ya bada Jan Kati guda 8 ga ƴan wasa mata 8 daban-daban.
Lokacin da ake tambayar sa me yasa yayi hakan, Sai ya bada amsa da cewa: Saboda kamata yayi ace Mata suna ɗakin Girki wajen dafa abinchi ba filin kwallo ba!
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ