Daga Aisha Salisu Ishaq
Ƴan bindigan da su ka sace Dakta Adekunle Raif Adeniji, Daraktan Gudanarwa na Sakatariyar Jam’iyyar APC a Abuja, sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 350 kafin su sako shi.
Alfijir labarai ta rawaito cewa iyalansa sun samu kira daga masu garkuwar, inda su ka dage cewa sai an biya kudin fansa kafin su sake shi.
Wani daga cikin iyalansa, da ya yi magana da wakilin Daily Trust jiya Talata, ya ce Daraktan da wasu mutane da aka sace tare da shi suna hannun masu garkuwar har yanzu, kuma sun ce ba za su sake shi ba har sai an biya kudin fansar.
Wata majiya a APC ta tabbatar da wannan batu ga jaridar Daily Trust.
An sace Dr. Adeniji makonni biyu da su ka gabata a yankin Chikakore da ke Kubwa, cikin Ƙaramar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja.
Daily Trust
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ