Dara Taci Gida: Ma’aikacin EFCC Ya Cika Wandon Sa Da  Iska A Kaduna

FB IMG 1706852279199

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na cikin tsaka mai wuya bayan da wani Ma’aikacin Hukumar yayi wata badakalar sama da dala 30,000 da wasu kayayyaki.

A farkon watan Jinairu, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta tsare jami’anta 10 a Legas bisa zargin satar wasu kayan aiki da ba za su iya tantance yawan su ba.

Ko da yake hukumar ba ta bayyana takamaiman abubuwan da jami’an ya sace ba, binciken Jaridar DAILY Nigerian ya nuna cewa sun saci zinare da suka haura Naira biliyan 1 da kuma sama da dala 180,000 da kuma kimanin wasu kayauyaki na 140,000.

A cikin sabuwar badakalar, rohoton ya nuna cewa wani ma’aikacin hukumar, mai suna Polycarp, ya yi batan dabo bisa zargin handame sama da $30,000.

Izuwa yanzu ana cigaba da neman jami’in Hukumar ruwa a jallo don girbar abinda ya aikata..

Wasu daga cikin wadanda suka nemi a sakaya sunansu sun shaida wa wannan jaridar cewa, darektan shiyyar, Benedict Ubi, makonni biyu da suka gabata, ya ba da umarnin a binciki daraktocin, sakamakon rikicin cikin gida da ya faru a Legas.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *