Ministan Ilimin Nijeriya Farfesa Tahir Mamman a wani sako ranar Juma’a ya bayyana cewa jami’o’i uku kawai Nijeriya ta amince da su a Benin, biyar a Togo.
Alfijir Labarai ta rawaito ministan Ilimin ya ce za a hukunta duk wani jam’in Nijeriya da aka samu da hannu wajen amincewa da shaidar digiri ta boge.
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta bankaÉ—o shaidar digiri ta bogi guda 22,739 daga jami’o’i a Jamhuriyar Benin da Togo. Ministan Ilimin Æ™asar Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja, yayin wani taron manema labarai.
Farfesa ya ce daga bayanan da ke hannun hukumar masu yi wa Ƙasa hidima (NYSC), an gano cewa “É—alibai 21,634 sun gabatar da shaidar digiri ta bogi daga Benin daga 2019 zuwa 2023.”
“Mun kuma gano shaidar digiri ta bogi 1,105 daga Togo,” in ji ministan.
Ministan ya ce Majalisar Zartarwa ta Æ™asa ta amince a kori waÉ—anda aka gano sun gabatar da shaidar karatu ta bogi daga Æ™asashen, waÉ—anda suke aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ya ce mutanen sun gabatar da shaidar digiri ne daga jami’o’in da Æ™asashen ba su amince da su ba.
Farfesa Tahir Mamman ya ce duk É—alibin da ya gabatar da shaidar digiri daga jami’o’in da ake koyarwa da Turancin Ingilishi daga shekarar 2017, to sakamakon bogi ya gabatar.
Ministan ya bayyana cewa duk ma’aikatan da aka samu da hannu cikin wannan badaƙala, suna fuskantar matakan ladabtarwa. Sannan sassan da ke kula da aikin, su ma ana yi musu garambawul.
Matakin na gwamnati ya biyo bayan wani bincike da wani É—an jarida ya yi, inda ya ce ya samu shaidar digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida, ba kuma tare da ya halarci jami’ar ba.
A watan Disambar 2023 ne, É—an jaridar na Daily Nigerian, Umar Audu, wanda ya yi basaja a matsayin É—alibi ya nuna shaidar digiri na bogi da ya samo daga Benin har ma kuma ya shiga sansanin Masu Yi wa Ƙasa Hidima a Naijeria da wannan sakamakon, bayan ya samu sahhalewar ma’aikatar ilimi.
Lamarinin ya É—auki hankali sosai a Nijeriya a lokacin, har ma gwamnati ta ce ta É—auki mataki don magance matsalar, wacce ake gani ta samu karÉ“uwa ne saboda haÉ—in bakin wasu jam’ian gwamnati.
TRT Afrika
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj