Dole APC Ta Fadawa ‘Yan Najeriya Yadda Kayi Da Dalar Shinkafar Gwamnatin Buhari – In Ji PDP

FB IMG 1709034735335

Jam’iyyar PDP ta bukaci jam’iyyar APC mai mulki da ta bayyana wa ‘yan Najeriya abin da ya faru da dala na shinkafa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a shekarar 2022.

Alfijir labarai ta rawaito Debo Ologunagba, sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, wanda ya yi magana a zantawarsa da jaridar TheCable a jiya Litinin, ya ce bukatar irin wannan bayanin ya zama dole saboda fama da yunwa da yanayin tattalin arzikin kasar a yanzu.

A makon da ya gabata ne dai aka ce mutane bakwai ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a yayin da hukumar kwastam ta Najeriya ta ke rabon buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 25 a Legas.

Kakakin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa, da ace jam’iyyar APC ta cika kasuwa da shinkafar da gwamnatin Buhari ta kaddamar da ba’a samu wannan cikowar ba.

“A makon da ya gabata, Hukumar Kwastam ta Najeriya tana sayar da shinkafar da aka kama kuma mutane bakwai sun mutu a Legas. Ta yaya muka kai wannan matakin? Sannan gwamnatin APC karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shaida mana cewa akwai wadataccen shinkafa a Abuja,” inji Ologunagba kamar yadda The Cable ta ruwaito.

“Idan da gaske ne an sami wadataccen abinci a baya, me ya sa ake fama da yunwa a ƙasar?

Ologunagba, wanda ya bukaci gwamnati da ta ayyana dokar ta baci kan yunwa, ya kara da cewa ya kamata gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta magance matsalolin rashin tsaro domin manoma su je gona.

“Ya kamata wannan gwamnati ta mayar da hankali kan rashin tsaro. Idan an tabbatar da tsaro a muhalli, mutane za su je gonakinsu, za a karfafa wa mutane tafiye-tafiye domin kasuwanci,” inji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *