An bukaci Shugaban kasa Tunibu da lallai ya maida ma’aikatar ciniki da masana’antu jihar Kano ko kuma Onisha, matukar ya maida ya maida hukumar dake kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya FAAN jihar Legas.
Alfijir labarai ta rawaito Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewa wato (Arewa Consultative Forum) Alhaji Bashir Dalhatu, SAN ya bayyana hakan ta cikin wata tattaunawa da gidan Talabijin na Arise.
Bashir Dalhatu ya ce, idan har Tunibu zai maida FAAN Legas saboda an fi zirga-zirgar jiragen sama, toh lallai ne ya maida ma’aikatar ciniki da masana’antu jihar Kano ko kuma Onisha, tunda anfi hada-hadar kasuwanci a wadancan wurare.
Haka kuma Tsohon ministan na makamashi da karafa ya kara da cewa, sai Tunibu ya kuma dauke ma’aikatar Ilimi ko ta Noma ya maida ita Makurdi, tunda can ne suka yi fice a fannonin biyu.
A dan haka yace ya zamar wa Shugaban kasa Tunibu wajibi ya karkasa dukkan ma’aikatun gwamnatin Tarayya zuwa wuraren da suka fi yin fice a kowanne fanni.
Toh sai dai yace Wannan ba shine manufar samar da Babban birnin Tarayya ba, domin kuwa anyi hakan ne, domin samar da hadin kai dama dunkulalliyar kasa.
Ya kuma yi martani dangane da dalilin da gwamnatin ta bayar na rashin isashshen wuri, inda yace an wuce wannan tsari na dole sai mutum yaje wurin aikin sa, tunda ana iya yin komai daga gida saboda canzawar zamani.
Tsohon ministan ya kuma ce, hakan na nufin idan wani Shugaban yazo daga Arewacin Najeriya sai shima ya dauki Babban birnin Tarayyar daga Legas ya mayar dashi Kaduna, kano, Sokoto ko kuma wata jihar ta Arewa.
A karshe yayi fatan Shugaban kasa Tunibu zaiyi duba na tsanaki akan lamarin, domin zai kawo maslahar kasa baki Daya.
GTR HAUSA
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V