Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), reshen Kaduna, ta kama wani tsohon ɗan kwangila da Gwamnatin Jihar Kaduna, Bashir Bello Ibrahim, wanda kuma shi ne Shugaban kamfanin Formal Act Legacy Limited, bisa zargin damfara da ya kai kimanin Naira biliyan 30.
EFCC ta bayyana cewa wanda ake zargin yana ci gaba da bayyana kansa a matsayin mai bada shawara ga dukkan kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna, da kuma kungiyoyi guda biyu masu zaman kansu — United Charity Foundation (UCF) da FICCORD — wadanda suka da’awar suna aiki tare da ofishin Sustainable Development Goals (SDGs). Wannan na faruwa ne duk da cewa gwamnatin jihar ta soke duk wata yarjejeniya da ta kulla da su tun a watan Oktoban shekarar 2023.
Rahotanni sun ce Ibrahim ya raba kwangiloli na bogi ga mutane inda yake karɓar kayayyaki kamar gadon asibiti, magunguna, injinan ruwan sha da wutar lantarki, ba tare da biyan masu kayayyakin ba. Haka kuma, binciken EFCC ya bankado cewa yana amfani da wasu mutane wajen siyar da takardun kwangila na ƙarya, inda daga bisani ake raba kuɗaɗen da suka samu.
A yayin da binciken ke cigaba, EFCC ta kwato wasu muhimman kayayyaki daga hannun wanda ake zargin, ciki har da motocin Hilux, ambulans, babura masu gadon asibiti, da magunguna masu yawa. Hukumar na aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna domin tantance ingancin kayan da aka kwato.
Sakamakon binciken masana, an tabbatar da cewa wasu daga cikin magungunan sun lalace, wasu kuma na jabun ne. Haka kuma, wurin da aka ajiye kayan bai cika ka’idojin lafiya ba wajen ajiya na irin waɗannan kayayyakin masu matuƙar muhimmanci.
EFCC ta ce za a gurfanar da Bashir Bello Ibrahim a gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da tabbatar da cewa ana cigaba da zurfafa bincike don gano yawan waɗanda suka shiga wannan zamba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD