EFCC Ta Gurfanar Da Matar Gwamnan Kogi Da Ɗan Uwansa Gaban Kotu

Alfijr ta rawaito  EFCC ta ce ta gurfanar da wasu makusantan gwamnan jihar Kogi a gaban kotu, ciki har da matarsa, Rashida Bello.

Hukumar tana zargin su ne da laifukan da suka shafi ɓarnata dukiya da halasta kuɗin haram na sama da naira biliyan uku.

A nata bangaren babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Mai shari’ah Obiora Egwuatu ta aike da tsare ɗan’uwan gwamnan mai suna Ali Bello a gidan gyaran hali da tarbiyya.

EFCC ta gurfanar da Abba A Dauda da Yakubu Siyaka, Adabenege da Iyada Sadat sai kuma Rashida Bello wadda EFCC ta ce tana neman ta ruwa a jallo.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *