Daga Aminu Bala Madobi
Tsohon Gwamnan Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace dakatar da Zababben Gwamnan Ribas hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar, El-Rufai ya bayyana cewa wannan mataki na Shugaban Kasa ba daidai ba ne, domin yana barazana ga tsarin dimokuradiyyar tarayya. Ya jaddada cewa kundin tsarin mulki bai bai wa Shugaban Kasa ikon korar zababbun shugabanni na jihohi ba.
Ya ce, “Ayyukan Shugaban Kasa suna da nauyi kuma suna da iyaka bisa tanadin kundin tsarin mulki da dokokin kasa, kuma ba su hada da korar mutanen da aka zaba ba.”
El-Rufai ya amince cewa lamarin tsaro a Jihar Rivers yana bukatar matakin gaggawa, amma ya ce kamata ya yi gwamnati ta ayyana dokar ta-baci domin bai wa hukumomin tsaro damar magance matsalar, ba wai rusa zababbun shugabanni ba.
Ya kuma tunatar da yadda Kotun Koli a shari’ar Dariye vs. Attorney General of the Federation ta bayyana cewa dakatar da zababbun jami’an gwamnati ba bisa ka’ida ba ne.
El-Rufai ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sake nazari kan wannan mataki, yana mai tunatar da shi cewa lokacin yana dan adawa, ya soki matakin da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya dauka na ayyana dokar ta-baci a Arewa maso Gabas.
Ya ce, “Bai kamata mu yi shiru ba yayin da muke ganin ana maimaita irin abubuwan da suka faru a dokar ta-baci ta Yankin Yamma a shekarar 1962.”
Daga karshe, El-Rufai ya bukaci ‘yan Najeriya masu kishin kasa da masu tunani mai kyau da su hada kai domin kare dimokuradiyya da bin doka da oda a kasar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD