Daga Aminu Bala Madobi
…Rantsar da mai rikon mukamin gwamna kafin Majalisa ta yanke hukunci karan-tsaye ne ga tanadin doka, janyo ce-ce-ku-ce.
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Na Cigaba Da fuskanta kalubalen samun rinjaye tun bayan kai kudirin ayyana dokar ta-6aci a jihar Ribas gaban Majalisun dokoki na kasa.
Rahotonni sun tabbatar dacewa an tafka zazzafar muhawara lamarin da ya kaiga ba a kaiga cimma wata matsaya ba kan kudirin ayyana dokar ta-6acin.
Kididdiga ta nuna cewa kafin kaiwa ga amince ayyana dokar ta-6aci, Wanda aka nada ya cigaba da aiki, ana bukatar kashi biyu cikin uku (2/3) na kuri’un Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar ta-baci da aka ayyana.
Sai dai, bisa ga adadin ‘yan majalisa na yanzu, jam’iyyar APC ba za ta iya cimma wannan rinjaye ba, ko da duk adadin ‘yan jam’iyyar ne suka kada kuri’a a goyon bayansa.
A Majalisar Dattawa, APC na da ‘yan majalisar Dattawa 58, PDP 37, Labour 7, SDP 2, NNPP 2, APGA 1, ADP 1, yayin da ake da kujera daya wadda babu kowa.
A Majalisar Wakilai kuwa, APC na da ‘yan Majalisu 175, PDP 118, Labour 35, NNPP 19, APGA 5, ADC 2, SDP 2, YPP 1, tare da guraben wakilci guda uku da babu kowa a kansu.
Doka ta tanadi cewa Majalisar Tarayya na da awanni 48 don tantancewa ko za a amince da dokar ta-baci ko kuma a yi watsi da ita, inda wa’adin hakan ke karewa a ranar Alhamis.
Sai dai, matakin da Shugaban kasa ya dauka na rantsar da mai rikon mukamin gwamna kafin Majalisa ta yanke hukunci ya janyo ce-ce-ku-ce.
Masana harkokin siyasa da ‘yan Najeriya da dama na tambayar irin sakon da Shugaban kasa ke kokarin aikawa da wannan mataki.
Wasu na ganin hakan tamkar take doka ne da tauye hurumin Majalisar Tarayya.
Yanzu dai ana jiran ganin yadda Majalisar Tarayya za ta dauki mataki kafin wa’adin tantancewar ya cika a gobe Alhamis.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD