EPL: ‘Yan wasan Man Utd sun fusata da yadda Kocinsu ya wulakanta tsohon abokin wasansu

Wasu manyan ‘yan wasan Manchester United sun fusata da kociyan kungiyar Erik ten Hag kan yadda aikin gola David de Gea ya kare da rashin girmamawa.

De Gea ya bar Old Trafford a bazarar nan bayan shekaru 12 a kulob din Premier.

Duk da cewa salonsa ya canza a matakin karshe na rayuwarsa ta United, dan kasar Sipaniyan ya lashe kyautar Golden Gloves a kakar wasan da ta wuce kuma an ba shi kyautar gwarzon dan wasan kungiyar sau hudu daban-daban.

Amma an fitar da Dea dan shekaru 32 ba yadda ya kamata, a wani salo na rashin yabawa sakamakon takaddamar kwangilarsa.

A cewar The Sun, yadda Ten Hag ya yi wa De Gea ya bar kungiyar, gungun ‘yan wasa suna yin alawadai kan yadda aka wulakanta abokin wasan nasu.

Shawarar dan kasar Holland na maye gurbin De Gea da Andre Onana bai taimaka masa ba a komai.

Ten Hag ya sanya wa Onana kan fan miliyan 50 daga Inter Milan, amma dan wasan na Kamaru ya sha wahala a farkon rayuwarsa ta United, domin ya kasa tabuka komai.

Onana ya sake tafka laifi a wasan da suka sha kashi a hannun Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba lokacin da kuskurensa ya ba Leroy Sane damar bude kwallon a ci 4-3 a gasar Bundesliga.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *