Tinubu ya shigar da karar gaggawa don hana jami’ar Chicago fitar da sakamakon karatunsa yau Juma’a

An shigar da buƙatar gaggawar ne yayin da Jami’ar Jihar Chicago ke shirin fara fitar da bayanan karatun a yau Juma’a da yamma.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban kasa Bola Tinubu ya shigar da karar gaggawa, yana neman a sake duba umarnin da mai shari’a ya bayar na a saki bayanan karatun sa ga Atiku Abubakar.

A ranar 19 ga watan Satumba mai shari’a Jeffrey Gilbert na kotun Amurka ya umurci jami’ar jihar Chicago da ta saki bayanan Tinubu ga abokin hamayyarsa na siyasar Najeriya a wani bangare na ci gaba da kalubalantar zabe a Najeriya.

Alkalin ya ce dole ne a mika bayanan ga Mista Abubakar a ranar 22 ga watan Satumba.

Ya kuma ce dole ne shugabannin makarantu su mika kansu don tabbatar da duk bayanan da aka fitar a karkashin rantsuwar doka.

Amma yayin da makarantar ta fara shirye-shiryen fitar da bayanan, Tinubu ya shigar da karar gaggawa a gundumar yana neman wani babban alkali da ya sake duba umarnin Mista Gilbert a ranar 19 ga Satumba, kuma ya jinkirta aiwatar da hukuncin har zuwa akalla 25 ga Satumba.

“Shirye shiryen Jami’ar Chicago na sakin bayanan ya gamu da tasgaro, yayin da lauyan Tinubu ya gabatar da wannan kudirin dabam na kalubalentar hukuncin da kotun Majistare zata yanke, karkashin jagorancin Lauya Christopher Carmichael.

Sai dai Mai shari’a Nancy Maldonado ta shirya sauraron karar da karfe 3:00 na rana yau juma a, cikin gaggawa.

Ana sa ran lauyoyin dukkan bangarorin Tinubu da Atiku, za su halarci zaman domin sauraron hukuncin.

Cikakkun bayanai daga baya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *