Fitattun Jaruman Kannywood 5 Da suka taba yin Takarar Siyasa A Kasar nan

Ko kunsan Cewar Jaruman Kannywood ma ba a barsu a baya ba wajen taka rawa a siyasar Nigeria

Akwai fitattun Jaruman Kannywood da suka Fito aka Fafata da su a kujeru mabambanta a jam iyyu daban daban.
1. Hamisu Lamido Iyantama
2. Alasan Kwalle Bakin wake
3. Abba El Mustapha Ruda
4. Nura Hussain Yasayyadi 
5. Lawan Ahmad Honorable 

Iyantama Yayi Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam iyyar N D Party a shekarar 2007.

Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano a Jam iyyar ANPP Shine ya kada iyantama Har kasa

Alasan Kwalle Takarar Shugaban Karamar Hukumar Ungogo a Jam iyyar P D P bai Sami nasara ba.

Daga Bisani ya sake Tsayawa 1akarar Kansila a Jam iyyar A P C a 2015.

Abba Ruda Shima ya tsaya Takarar Dan Majalisar Jaha a Jam iyyar P D P a karamar Hukumar Gwale shekarar 2015. Shima Bai Sami Nasara ba. 

Nura Hussain Shima ya Fito Takarar Kansila a Karamar Hukumar Birnin Kano Mazabar Yakasai a shekarar 2007, Shima bai Sami Nasara ba. 

Lawan Ahmad Shima ya Tsaya Takarar Dan Majalisar Jahar Katsina Karamar hukumar Bakori a Shekarar 2019, Shima bai Sami Nasara ba.

Wannan ta tabbatar da cewar Jaruman Kannywood suma ba a barsu a baya ba wajen siyasar Kasar nan. 

Slide Up
x