Ganduje, Matawalle Da Wasu Ka Iya Rasa Kujerun Ministocin Tinubu

Daga Aminu Bala Madobi

Da akwai alamu masu karfi dake cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki su sha kaye, kamar yadda rahotanni suka ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya amfani da dukkan zarge-zargen tsaro da na cin hanci da rashawa wajen yanke hukunci kan ministocinsa.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban kasa a yunkurinsa na cika wa’adin ne, a yau Lahadi ya cika kwanaki 48 da hawansa mulki, tuni ya aika da wasu sunaye ga hukumomin tsaro domin tantancewa gabanin mika sunayen ministoci ga majalisar dattawa kafin ranar Alhamis 27 ga watan Yuli. 2023.

A ranar 27 ga watan Yuli ne ‘yan majalisar dattawa za su tafi dogon hutu, amma rashin gabatar da sunayen ministocin nasa ka iya jinkirta hutun nasu.

Wata majiya ta ce Shugaban kasa, maimakon kin amincewa da su, zai yi amfani da rahotannin don zabar mara sa lefuka domin nada su ministoci a gwamnatin sa.

An ce tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya mayar da fadar shugaban kasa tamkar gidansa tun bayan da ya bar mulki a matsayin gwamna na iya kasancewa cikin wadanda za a ki amincewa da nadinsa saboda zarginsa na cin hancin bidiyon dala da Kano ke bincike a halin yanzu.

Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle shi ma za a iya cire shi bisa zargin damfarar N70bn da EFCC ta yi masa.

Rahotanni sun ce Tinubu na yin haka ne domin jam’iyyun adawa kamar NNPP, APGA, da sauran su su samu mukamai a matsayin minista.

Wannan kuma wata hikima ce a shirin Tinubu na kafa gwamnatin hadin kan kasa ya tabbata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

3 Replies to “Ganduje, Matawalle Da Wasu Ka Iya Rasa Kujerun Ministocin Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *