Ganduje Ya Bayyana Dalilan Cire Sunan Maryam Shetty Daga Cikin Ministoci

Lokacin da aka bayyana sunanta, mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai, ka san kuma wadannan kafafen na da tasiri sosai.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, kuma tsohon gwamnan jihar kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce surutan da mutanen jihar Kano suka rika yi a kafafen sada zumunta kan nadin Maryam Shetty ne suka sa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya canza shawararsa a kan nada ta minista.
An dai yi ta zargin cewa Ganduje, ne ya taka muhimmiyar rawa wajen cire sunan Maryam din da kuma maye gurbinta da na Mariya Mahmoud Bunkure wacce tsohuwar Kwamishiniya ce a tsohuwar gwamnatinsa.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa dake Abuja, Ganduje ya ce surutan da aka rika yi ne suka canza tunanin Tinubu akan Maryam Shetty.

“Lokacin da aka bayyana sunanta, mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai, ka san kuma wadannan kafafen na da tasiri sosai.

Sai Shugaban Kasa ya kira ni ya tambaye ni, ku kuka bayar da sunanta, na ce masa a’a” a cewar Ganduje

“Sai ya tambaye ni ko na santa, na ce ban santa ba, sai ya ce to yaya aka yi aka shigar da sunanta in ba daga wajenku yake ba?

“A nan ya janye sunanta, inda ya nemi shawarar wacce zai maye gurbinta, tun da dole ya ce mace yake so, sai muka ba shi sunan Dokta Mariya, tun da akalla ita mun yi aiki da ita, kuma mun san kwarewarta”. Inji Ganduje

Ganduje yace wajen zabarta, sun yi la’akari da yankin da ta fito na Kano ta Kudu, wanda ya sha korafin cewa a baya ana danne shi, “ka ga yanzu mun yi adalci ke nan.

Sai dai ya ce duk da haka, yana da kwarin gwiwar Shugaban Kasa ba zai bar Maryam din haka ba, zai ba ta wani muƙamin a nan gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *