Ganduje ya fara karbar ƴan Kwankwasiyya da suka canza sheka zuwa APC

Shugaban jam’iyyar APC na kasa a Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi dan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Bauchi a zaben 2023, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Alfijir Labarai ta rawaito Ganduje ya yaba wa shawarar Haliru Dauda Jika ta koma wa jam’iyya mai mulki, a matsayin wani mataki da ya dace, inda ya nunar cewa tabbas a yanzu tsohon dan takarar na NNPP ya gane cewa jam’iyyar NNPP “mai samun goyon bayan Kwankwasiyya, yaudara ce da ci da gumi”.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa da yake karbar Haliru Jika da illahirin shugabannin jam’iyyar NNPP a Bauchi, Ganduje ya ce “Lokacin da na samu labarin cewa za ka zo ganina don tattaunawa a kan hanya mai bullewa, na san na hadu da wani jigon dan siyasa, wanda kowa ya san shi a Bauchi”.

“Ya dawo zuwa jam’iyyar masu ra’ayin ci gaba da kuma alkibla, musamman ganin inda ya baro. Ya taho daga wata jam’iyya wadda a baya ta kasance mai daraja da matukar kima, amma daga baya sai Kwankwasiyya ta karkatar da ita, ta gurbata ta.

“Muna farin cewa NNPP ta ainhi ta dawo kuma ta hau kan cikakken matsayinta, inda ta yasar da kungiyar Kwankwasiyya, duk ta yi watsi da ita gaba daya.

“An tilasta wa kungiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano tafiya hutu tsawon shekara takwas, kafin ta sake komawa Gidan Gwamnati.

Shugaban APC ya kuma yi wa ‘yan siyasar da suka koma jam’iyyar tasa alkawarin shigar da kowa a dama da shi cikin tafiyar jam’iyyar a jihar Bauchi, a wani bangare na kokarin sake fasalin APC kafin zaben 2027, inda ya nanata cewa jam’iyyar ta yi nadama kan rawar da ta taka a Bauchi, yayin zabukan da suka wuce.

Tsohon dan takarar na jam’iyyar NNPP ya bayyana wa manema labarai cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda muradan dumbin magoya bayansa a jihar Bauchi. Ya ce, “jingine tafiyar NNPP da na yi zuwa APC, ba shi wata alaka da dan shugaban kasa na jam’iyyar. Ba ni da wani sabani da Kwankwaso”.

BBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *