Ganduje ya raba kujerun Hajji da motoci ga daliban da suka shiga Musabaqar a Kano

FB IMG 1732824553953

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero sun jagoranci bikin rufe musabaqar Al-Qur’ani mai girma wanda gidauniyar raya addinin musulunci ta Ganduje foundation take daukar nauyi shekara-shekara.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban jam’iyyar wanda kuma shi ne Shugaban gidauniyar ya raba kujerun Hajji da motoci da babura masu kafa uku ga wadanda suka lashe gasar karatun sahun farko, inda kuma ya raba babura masu kafa biyu da kekunan dinki dana hawa da sauran kyaututtuka ga sauran wadanda suka lashe gasar.

Gidauniyar Ganduje foundation cibiya ce da ta shafe sama da shekaru talatin (30) wajen hidimtawa addinin musulunci da taimakawa al’umma wanda ya hada da gina masallatan juma’a da gina makarantun Islamiyyu da musuluntar da maguzawa da Kuma yiwa masu larurar idanu aiki kyauta.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ana shirya Musabaqar ne don zaburar da yara da matasa koyon karatun Qur’ani da bin ka’idojin sa da sanin ma’anar sa da kuma yiwa daliban ilimi kaimi domin su kara maida hankali wajen karatun Qur’ani.

Kotu ta jingine hukunci a shari’ar kuɗin ƙananan hukumomin Kano

A wata sanarwa da hadimin Ganduje Aminu Dahiru ya aikowa kadaura24, ya ce Manya malamai daga sassa daban-daban na kasa ne da daliban ilimi da sauran muhimman mutane ne suka samu damar halartar taron.

Shugaban kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da dan takarar mataimakin gwamnan Kano a shekarar 2023 Alhaji Murtala Sule Garo da Hajiya Asiya Abdullahi Ganduje na daga cikin wadanda suka mika kyaututtuka ga gwarazan musabaqar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *