Zamu haɗa kai da sauran gwamnonin Arewa da yan majalisu domin yakar ƙudirin dokar sabon haraji – In ji Gwamna Zulum

Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatinsa tare da goyon bayan sauran gwamnonin Arewa za su hada kai da ‘yan majalisun dokoki daga yankin arewacin Najeriya don yakar sabon kudirin dokar haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke son gaggauta amincewa da shi. 

A wata hira da BBC, Zulum ya bayyana cewa kudirin dokar zai kara wa jihar Legas karfi a tattalin arziki, yayin da zai durkusar da yankin Arewa. Ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta matsa lamba kan ‘yan majalisa don su amince da dokar ba, musamman duba da yadda aka gaggauta tura kudirin. 

Zulum ya yi gargadi kan wannan hanzari, yana mai cewa: 

“Akwai kudirori da suka shafe shekaru ana jayayya a kansu kafin su zama doka. Me ya sa a wannan lokaci ba za a natsu ba, a fahimci wannan kudiri sosai kafin a amince da shi?” 

Gwamnan ya kara da cewa kudirin ya saba wa muradin jama’a da dama daga kudu da arewa. Har ila yau, ya bayyana cewa wasu daga cikin shiyyoyin kudancin Najeriya kamar Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Kudu ma ba sa goyon bayan dokar. 

Gwamna Zulum ya yi kira ga wakilan Arewa da su farka domin kare muradun yankin kafin lamarin ya kazanta.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *