Ganduje Ya Yi Martani Kan Sammacin Muhyi Magaji Rimin Gado

Tsohon gwamna Ganduje ta bakin Kwamishinansa na harkokin raya karkara da ci gaban al’umma, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya mayar da martani dangane da wannan sabon yunkuri na hukumar yaki da rashawar ta Kanon.

Alfijir Labarai ta rawaito Musa ya bayyana cewa, “Tun shekaru biyu zuwa uku da suka gabata tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika wannan batu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kuma yanzu haka maganar tana kotu, don haka bai kamata a ce wani ya yi sammaci ya ce yana bincike akan lamarin dake gaban kotu”

A hannu guda kuma, kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari sun fara tofa albarkacin bakin su game da batun, inda Kwamared Ibrahim Garba Maryam, mamba a zauren gamayyar kungiyoyin na jihar Kano ya ce, “abinda ya kamata mutane su gane shi ne lokacin da wannan abu ya faru shi gwamna yana da kariyar doka, yanzu kuwa babu wannan kariya don haka dole yanzu doka ta yi aiki a kansa a yi bincike, amma idan za a yi bincike tilas ne a yi bisa adalci.

“Shi cin hanci da wanda ya bayar da wanda ya karba duk suna ciki, saboda haka ina wanda ya bayar din? Ina kamfanonin da suka yi aikin? Ya kamata a hada dasu.”

Baya ga kungiyoyin fararen hula, masu sharhi a fagen siyasa da harkokin yau da kullum a jihar ta Kano na ci gaba da bayyana fahimtar su a kan lamarin.

Alhaji Jafar Sani Bello daya daga cikin masu fashin baki akan siyasa da al’amuran yau da kullum a Najeriya ya ce “Ni a gani na Muhuyi ya saki damarsa ta bincikar gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin kuwa al’amarin ya faru lokacin yana kujerar shugabancin hukumar Rashawa ta Kano, amma bai ce komai ba kuma daga bisani suka yi fada har gwamnan ya sauke shi daga kujerar.

Don a yanzu ba zai iya yin adalci ba ga tsohon gwamnan saboda ta yiwu a akwai gilli a zuciyar sa.”

Tun a shekara ta 2018 ne aka fara ce-ce-ku-ce akan wannan fefen bidiyo wanda mawallafin jaridar kafar Intanet ta Daily Nigerian wato Jafar-Jafar ya fara kwarmatawa lokacin da ake tunkarar zaben 2019, koda yake batun ya lafa daga bisani, amma masu kula da lamura na ganin sake bude shafin maganar ba zai rasa nasaba da kammala wa’adin mulkin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba da kuma yadda siyasar Kanon ke ci gaba da daukar sabon salo.

Aminiya/VOA Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Slide Up
x

2 Replies to “Ganduje Ya Yi Martani Kan Sammacin Muhyi Magaji Rimin Gado

  1. Gaskiya mutane suna da sonzuciya mutuminnan barawone duniya ta sani amma meye dalilin dayasa baza a harbeshiba saboda ni anawa ra’ayin duk wani me mukami nagwamnati gwamna ko shugaban kasa komawaye idan aka kamashida satar kayan gwamnati ko cin hanci dame karbar dawanda yabayar hukuncinsu dayane ko a harbesu, ko kuma ayimusu irin daurin da akayiwa mejo Hamza Almustafa.wannan Shine ra’ayina, Babba Ja’oji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *