Ganduje Yace Sabbin Masarauta Kano Zama Daram Ba Za Su Rushe Ba

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kirkiro sun zo kenan ba rushewa.

A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso, ya yi nuni da cewa gwamnati mai jiran gado za ta yi nazari a kan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, da kuma rarraba masarautar.

Amma yayin da ya ke jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta 2023 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano a yau Litinin, Ganduje ya ce Allah ba zai kawo wanda zai rusa masarautun ba.

A cewarsa, masarautun sun kawo ci gaba, hadin kai, da jin dadin al’ummar Kano.

Gwamna Ganduje ya ce, “Duk wanda ya ziyarci hedikwatar wadannan sabbin masarautun zai yarda cewa mun kawo ci gaba a wadannan wuraren.

“An kirkiro wadannan masarautu ne domin hadin kai, ci gaba, tarihi, da kuma dawo da martabar sarautar gargajiya. Mun ƙirƙire su ne don girmama mutanen wadannan yankuna.

“Ina so in tabbatar muku da cewa wadannan masarautun na dindindin ne, zama daram.

Kuma duk wanda zai rushe su, Allah Ta’ala ba zai kawo shi jihar Kano ba.

Muna tabbatar muku da cewa an ƙirƙire su ne saboda ku, saboda ci gaban ku.

“Ko ba ma gwamnati, muna addu’a kuma za mu ci gaba da addu’ar Allah ya kare wadannan masarautun daga dukkan sharri. Na gode muku duka,” inji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “Ganduje Yace Sabbin Masarauta Kano Zama Daram Ba Za Su Rushe Ba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *