Ma’aikatar Ƙasa da Safiyo ta jihar Kano, ta ce za ta buga sunayen wadanda su ka ki sabunta takardun shaidar mallakar gidaje da filaye a karkashin shirin sabuntawar da ta kwashe watanni ta na gudanarwa.
Kwamishinan ma’aikatar, AbdulJabbar Garko ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a taron manema labarai a Kano a yau Talata.
Ya ce baya ga jaridun na kasa, za a buga sunayen wadanda suka gaza a dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala da kuma Babbar Kotun Jihar Kano, domin a sanar da daukar matakin da ya dace.
Ya kuma sanar da karin wa’adin rufe yin rijistar zuwa watanni biyu, inda ya yi gargadi cewa duk wanda ya gaza sabunta takardun to fa gwamnati ba ta da wani zabi illa ta karɓe takardun kadarar ta sa.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD