Daga Aminu Bala Madobi
Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 wanda ya haura naira tiriliyan 1.47, lamarin da ke nuna girman kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da bunkasa ayyukan raya kasa da jin dadin al’umma.
Gwamnan ya amince da kasafin kuɗin ne a yayin zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano karo na 35 da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tafiyar da mulki da ci gaban jihar.
Kasafin kudin na shekarar 2026 na dauke da manyan tsare-tsare da aka tanada domin bangarorin ilimi, lafiya, noma, da gine-gine, tare da burin samar da ayyukan yi da rage radadin rayuwa ga al’ummar jihar.
Zaman majalisar ya gudana ne karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Ismail Falgore, inda aka jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da aiwatar da kasafin cikin gaskiya, adalci da rikon amana.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t