Wani babban jigo a jamiyyar APC ta jihar Adamawa Abdurrahman Haske yayi kira ga matasa na karamar hukumar Lamurde da su guji tayar da fitina da kuma tabbatar da tsarin nan na matsayin su na masu tabbatar da zaman lafiya.
Abdurrahman Haske yayi kiran ne lokacin da yake mika kayan tallafi ga wadanda rikici ya rutsa da su a wasu bangarori na karamar hukumar ta lamurde.ya kara da cewa tabbatar da zaman lafiya kuduri ne na kowa da kowa domin cigaban tattalin arziki da zamantakewa.
Haske ya kara da cewa matasa Allah ya hore musu iya kirkire- kirkire da kuma yawan da zasu kawo canji a cikin al’ummar su,sannan ya gargade su da cewa hazakar da suke da ita wasu ka iya amfani da su domin haddasa fitintinu.
“Young people must understand that violence only sets communities backward. Those who instigate unrest often disappear when the consequences arrive, leaving the youth and the wider community to suffer the losses,” Haske cautioned.
“Ya kamata matasa su gane cewa tayar da fitina yana sa al’umma koma baya kuma wadanda suka saka su suna janyewa su bar su da alumma.
Dan siyasar ya Kara da cewa ya kamata a gane cewa tattaunawa da Kuma fahimtar juna na taimakawa wajen magance matsalolin al’umma Wanda koma bayan hakan na jawo tashin hankali da rashin tsaro.
Haske ya kara da cewa raba kayayyakin ba wai kawai dan jinkai ba ne aa wata dama ce ta tabbatar wa da yan yankin cewa yana tare da su a kowanne lokaci.
Sannan Abdurrahman Haske yayi kira ga iyaye da kuma masu rike da mukaman gargajiya da su yi kokari wajen tarbiyyanyar da matsa wajen cusa musu hakuri girmamawa da Kuma zaman lafiya.
Sannan haske yayi kira da a zauna lafiya da samun hadin Kai a yankin na Lamurde domin cimma burin da aka
saka a gaba.
Ina kira da al’ummar yankin Lamurde da su zauna lafiya da hada kai wanda a hakan ne zaa gina zaman lafiya da kuma cigaba.
Al’ummar yankin na Lamurde sun jinjinawa dan siyasar Malam Abdurrahman Haske domin daukin da ya kawo musu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t