Gwamna Ganduje Ya Nada Sabbin Permanent Sakatare Guda 12 A Kano

Alfijr ta rawaito Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya amince da nadin sabbin Permanent Sakatare sakatarori guda 12 a ma’aikatan jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba a Kano, ta hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar.

A cewar Anwar, nadin zai fara aiki nan take.

Ganduje ya bayyana cewa nadin da jami’an za su yi zai tabbatar da samar da ingantacciyar hidimar jama’a a jihar a wannan zamani na bin ka’idojin da suka dace a duniya.

“Sabbin Permanent sakatarorin da aka nada sun nuna bajintar su wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

“Mun yi imani da karfin su, yayin da aka yi amfani da bincike mai zurfi da bincike a cikin tsarin zaben,” in ji shi.

Wadanda aka nada sun hada da Mansur Yakubu, Dan Azumi, Dr Sa’adatu Bala, Ahmad Abdullahi, Baba Dala, da Aliyu Garo.

Sauran sun hada da Abbas Sanusi, Dr Tijjani Hussain, Yahaya Amasaye, Aisha Kailani Mustapha Huguma, da Musa Garko.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *