Wata Kotu Ta Raba Auren Wata Masifaffiyar Mata Da Mijinta

Alfijr
Alfijr ta rawaito wata kotun majistare da ke zamanta a Ado Ekiti ta raba auren Ibrahim Idris da matarsa Bosede kamar yadda ya nema.

Ibrahim ya bukaci kotu ta raba auren ne saboda rashin girmama shi da kuma masifar da take masa, ga rashin samun kwanciyar hankali sannan uwa uba bata daukar gyara a al amuranta, kan abun da bai taka kara ya karya ba sai ta hau shi da fada ko barazana da rayuwa.

Alfijr

Ya kara da cewar ina iya kokarina wajen sauke hakkokin da suka rayata a kaina

Sannan ina rokon kotu da ta barin min ‘ya ta a hannuna saboda ta tashi a cikin Musulunci, kuma ta rika zuwa makarantar Islamiyya, kamar sauran ‘ya’yana,” inji magidancin.

A nata bayanin Bosede ta karyata duka zargin da maigidanta Idris ya gabatar wa kotun kan cewar shifcin gizo ne kawai.

Alfijr

Alkalin kotun, Misis Foluke Oyeleye ta kashe auren ma’auratan, bayan cikakken nazari data yi akan karar

Mai shari’a ta umarci mahaifiyar da ta ci gaba da kula da yar tasu, sannan ta umarci mahaifin ya dauki nauyi ‘yar tasu, kama makarantar boko da Islamiyya, kuma duk wata zai dinga bawa mahaifiyar dubu 10,000 don siyan abincin yarinyar.

Alfijr

A karshe, Bosede ta roki kotun a kan ta kwato mata wasu kayayyakinta da ke hannun Idris tun da aurensu ya mutu.

(NAN)

Slide Up
x