Gwamnan Kano ya amince da sayen taki na Naira biliyan 5 don manoman jihar

FB IMG 1716493752959

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sayan taki na kimanin Naira biliyan 5.07 domin tallafawa kananan manoma a jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito wannan yunkuri na da nufin saukaka wadatar abinci a matsayin sabon tsarin ci gaban noma a jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano a yau Talata, an ba da amincewar ne yayin taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 15, SEC.

โ€œZa a raba takin ne a fadin kananan hukumomi 44 domin tallafa wa manoma musamman na karkara domin kara yawan amfanin gona a kakar damina ta 2024,โ€ inji shi.

Ya bayyana cewa za a sayar wa manoman takin ne a kan farashi mai rahusa, wanda hakan ke nuna aniyar gwamnan na samar da kayan amfanin gona masu inganci da araha.

Wannan matakin ya biyo bayan siyan hatsi na biliyoyin naira a baya da gwamnan ya yi, inda aka raba wa marasa galihu a jihar domin rage raษ—aษ—i.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *