Gwamnan Kano Ya Bada Umurnin Kama Duk Wanda Ya Fito Zanga-Zanga A jihar

FB IMG 1716493752959

Gwamnan jihar Kano ya sanya takunkumi mai tsauri kan duk wani taron jama’a da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar, tare da yin amfani da ikon da aka bashi a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.
 
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, kuma aka aikawa da Alfijir Labarai.
 
Sanarwar ta ce, bisa ga matsayinsa, gwamnan ya umarci ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, da hukumar tsaro ta Civil defense ta Najeriya da su kama, tsare, da gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano. .
 
Wannan ƙwaƙƙwaran mataki dabara ce ta riga-kafi da nufin kawar da duk wata yuwuwar tabarbarewar doka da oda da maƙiyan jihar suka shirya. In ji sanarwar.
 
“Muna samun sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin kungiyoyin dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa maso Yamma domin tada hargitsi a fake da cewa suna goyon bayan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero. .”
 
Gwamnatin jihar ta fito karara ta haramta zanga-zanga ko jerin gwano ko wace iri ce, kuma za a kama mutanen da aka samu a kan titunan Kano suna yin irin wadannan ayyuka nan take.
 
“Ta wannan sanarwar, muna gargadin kungiyoyin dalibai da su guji yin amfani da masu tayar da kayar baya wadanda suka jajirce wajen tada rikici a Kano.”
 
Gwamnan ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya, kuma gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin don gaggauta maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da jihar ke samu a halin yanzu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *