Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar.

Screenshot 20240716 191123 WhatsAppBusiness

A yammacin ranar Talata gwamnan ya sa hannu kan dokar, sa’o’i kadan bayan majalisar dokokin jihar ta amince da dokar masarautun.

Alfijir labarai ta ruwaito Gwamnan ya sanya hannu ne kwanaki 51 bayan gwamantinsa ta rushe masarautu biyar masu daraja ta daya da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a jihar.

Masarautun masu daraja ta daya da aka rushe su ne na Bichi, Gaya, Kano, Karaye da Rano, aka dawo da tsohuwar masarautar Kano, wadda a yanzu Sarki Muhammadu Sanusi II yake jagoranta.

Dokar da majalisar ta amince da ita a safiyar Talata ta nada sarakuna masu daraja ta biyu a sabbin masarautun Gaya, Karaye da kuma Rano.

Dokar ta sanya kananan hukumomi takwas a karkashin sabbin masarautun.

Masarautar Rano ta ƙunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya.

Masarautar Gaya ta ƙunshi kananan hukumomin Gaya, Albasu da  Ajingi.

Ita kuma Masarautar Karaye ta ƙunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Duk sarakunan masarautun za su kasance a karkashin Sarkin Kano kuma za su kasance a matsayin abokan shawararsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *