Gwamnan Kano Ya Sauke Shugaban Hukumar Tattara kudaden Haraji (KIRS) Dambo Ya Nada Wani

FB IMG 1713292953070

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Dr. Zaid Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS).

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan ya kuma amince da nadin Kassim Ibrahim a matsayin daraktan zartarwa na hukumar tara kudaden shiga.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce sabon tsarin gudanarwar zai fara aiki nan bada dadewa ba yayin da tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Kano Alh. Sani Abdulkadir Dambo ya koma aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *