Gwamnan Katsina Ya Amince Da Fitar Da Biliyan N7.8bn Domin Sayen Kayan Aikin Tsaro

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya amince da fitar da zunzurutun kudi har kusan naira biliyan takwas da za a yi amfani da su don sawo kayayyakin aikin samar da tsaro na zamani don inganta tsaron al’ummar jihar Katsina.

Alfijir Labarai ta rawaito kwamishinan lamuran tsaron ciki gida na jihar Katsina Dr Nasir Mu’azu Danmusa, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gidan Gwamnatin jihar Katsina bayan sun kammala zaman majalisar zartarwa na jihar wanda gwamma Dikko Radda ya jagoranta.

Gwamnatin jihar Katsina za ta kashe N7,813,423,560.83 domin sayen sabbin kayayyakin aikin tsaro na zamani da za a raba wa jami’an tsaron dake aiki a jihar Katsina don ganin Gwamnatin ta inganta rayuwar al’ummar wajen samar da tsaro da zaman lafiya.

Idan za a iya tunawa dai jihar Katsina ta dade tana fama da harin yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, wanda hadan ya ke haifar da dardar a bin wasu daga cikin hanyoyin yankunan jihar.

Allah ya kawo mana lafiya da zama lafiya a yankunanmu na Arewacin Nijeriya dama kasa baki daya ameen.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *