Gwamnan Sokoto Ya Raba Gudunmawar Kudi Sama Da Miliyan 100 Ga Yan kasuwar Da Suka Yi Gobara A Jihar

FB IMG 1719121065834

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, ya bada tallafin tsagwaron kudi sama da Naira miliyan 100 ga masu sayar da babura da suka yi gobara a watannin baya a babbar kasuwar Sokoto.

Alfijir labarai ta ruwaito hakan dai ya fito fili ne lokacin da gwamnan ke raba tallafin na sama da Naira Miliyan 100 ga wadanda ibtila’in ya afkawa.

Da yake jawabi a wajen raba tallafin, shugaban kwamitin da gwaman jiha ya kafa don gano musabbabin gobarar tare kuma da bada shawara ga gwamnati akan matakin da ya kamata a dauka, Ambassador Sahabi Isa Gada yace, an kasa bada taimkon ne a rukuni rukuni tare da laka’ari da irin yawan hasarar da Yan kasuwar suka yi.

Wadanda suka fi samun babbar hasara sun samu sama da naira Miliyan 19 kowannen su, inda wadanda suka samu karamar hasara suka samu naira 300,000 kowannen su.

Alh. Sahabi ya Kara da cewa kwamitin nasu yayi aiki tukuru wajen ganin yabi diddigin wadanda ibtila’in gobarar ya shafa.

Ya kara da cewa sun zagaya wuraren da gobarar ta auku domin daukar sahihan bayanai akan wadanda lamarin ya shafa.

Shugaban ya ce tallafin kudin da gwaman jiha ya baiwa Yan kasuwar ba wai diyya bane, face dai tallafi ne don rage musu zogi da radadi na hasarar da suka yi don su kuma  sake kulla jari.

Hakazalika ya kuma bukaci yan kasuwar da suka amfana da tallafin,dasu yi cikakken amfani da kudaden da suka samu ta hanyar da ta dace.

A jawabin sa shugaban kungiyar masu sayarda baburan Alhaji Garba Gwazi ya jinjinawa gwamnan akan wannan taimkon da yayi musu, Wanda ya nuna irin so da kauna da kuma kulawa da gwamnan kewa alummar jihar nan.

Haka ma ya godewa sanator Aliyu Magatakarda wamakko akan irin gudunmawar da yake badawa ga wannan gwamnati na ganin cewa tayi koyi da salon  shugabanci irin nashi.

Garba Gwazi ya kuma bada tabbacin cewa zasu yi cikakken amfani da tallafin kudaden don bunkasa kasuwancin su.

FB IMG 1719121099518 1
📸 sokoto Gov

Abubakar Bawa, Sakataren hulda da yan jarida a fadar gwamnatin jihar Sokoto shine ya sanyawa sanarwar hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *